ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Saturday, November 14, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yadda Ciwon ‘Glacoma’ Ke Haddasa Makanta

by Sani Anwar
3 years ago
Glacoma

Mutane da dama na kamuwa da ciwon ‘Glacoma’ ba tare da sun sani ba, shi ya sa yake da mutukar muhimmanci da zarar mutum ya ji wani abu da ke nuna alamun ciwon ido, ya yi maza ya garzaya zuwa asibiti.

Har ila yau, ‘glacoma’ wata cuta ce wadda take kama idanu, ta sa ganin mutum ya samu matsala, wanda hakan kan jawo makanta. Kazalika wannan cuta, mafi yawancin lokaci ta fi kama masu shekaru, wadanda shekarunsu suka haura 40.

  • Manoma 40,000 Za Su Amfana Da Takin Zamani Na Bunkasa Noman Rani A Filato
  • Magance Bushewar Tafin Hannu A Lokacin Bazara

Sannan, idan akwai masu wannan cuta a gidanku ko a danginku, akwai barazana ko yiwuwar kamuwa da ita. Don haka, da zarar ka fara yawan jin kaikayi wanda ba ka saba ba ko ciwon ido, ka yi maza ka garzaya zuwa asibiti.

ADVERTISEMENT

Haka zalika, masu fama da hawan jini da kuma wadanda suka jima suna shan sha-ka-fashe, su ma akwai barazana tare da yiwuwar kamuwa da wannan cuta a tare da su.

Haka nan, babu shakka gaske ne ba a warkewa daga wannan ciwo idan ya yi kamari ko ya ta’azzara, amma idan aka garzaya asibiti da wuri kafin ciwon ya gama yi wa mutum illa, za a iya taimaka masa wajen rage karfin ciwon ta hanyar ba shi magunguna, domin ka da mutum ya makance.

LABARAI MASU NASABA

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

Har wa yau, yadda mutum zai san ya na da wannan ciwo na ‘glacoma’ shi ne, idan ya ga yana yawan yin ciwon ido ko ya ga  ba ya gani sosai ko ya rika ganin hawaye na fita a idanuwansa ko kuma ya ga idanun nasa yana yin ja.

Shi yasa yana da kyau idan mutu ya ji idanunsa na yin ciwo, ya yi maza ya garzaya asibiti domin a duba a ga mene ne yake damun sa, dalili kuwa wani lokacin za a iyayin zaton ko ciwo ne da aka saba yi yau da kullum a ki zuwa asibitin, ba a san cewa wannan ciwo ba ne da ka iya haddasa makanta ko wani abu mai kama da haka, Allah ya kiyaye mu; amin.

Glacoma
Sani Anwar
+ postsBio
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    MDPCO Ta Soki Ƙaddamar Da Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu A Kaduna
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Shirin Sulhu Tsakanin Kwankwaso Da Abba: Ina Aka Dosa?
  • Sani Anwar
    https://hausa.leadership.ng/author/sani-anwar/
    Ko Kun San Amfanin Kwanciya Da Bangaren Hagu?

MASU ALAKA

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha
Kiwon Lafiya

Amfanin Yawan Shan Ruwa Da Illolin Rashin Yawan Sha

November 1, 2026
Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin
Labarai

Uwa Da Jaririnta Sun Sha Da Ƙyar Daga Wata Mummunar Gobara A Ilorin

October 31, 2026
Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya
Kiwon Lafiya

Yadda Talauci Ya Sa Mutane Komawa Amfani Da Magungunan Gargajiya

October 31, 2026
Next Post
Gasasshen Nama Mai Dankali

Gasasshen Nama Mai Dankali

LABARAI MASU NASABA

An Yi Wa Shugaban Ƙasa Tinubu Ihu Bayan Sallar Juma’a

An Yi Wa Shugaban Ƙasa Tinubu Ihu Bayan Sallar Juma’a

November 14, 2026
Dangote Ya Fara Shirin Samar Da Wutar Lantarki Megawatt 10,000

Dangote Ya Fara Shirin Samar Da Wutar Lantarki Megawatt 10,000

November 14, 2026
Shugaban INEC Zai Bayyana Gaban Majalisa Kan Shirye-shiryen Zaɓen 2027

Shugaban INEC Zai Bayyana Gaban Majalisa Kan Shirye-shiryen Zaɓen 2027

November 14, 2026
Maaikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gabatar Da Burin Sin Dangane Da Kwarya-Kwaryar Taron Shugabannin APEC Dake Tafe

Maaikatar Harkokin Wajen Sin Ta Gabatar Da Burin Sin Dangane Da Kwarya-Kwaryar Taron Shugabannin APEC Dake Tafe

November 13, 2026
Kerry: Ya Kamata Amurka Da Sauran Kasashe Su Bi Sahun Sin Wajen Bunkasa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

Kerry: Ya Kamata Amurka Da Sauran Kasashe Su Bi Sahun Sin Wajen Bunkasa Amfani Da Makamashi Mai Tsafta

November 13, 2026
Baje Kolin Nuna Hotuna Tsakanin Sin Da Afrika Na Zurfafa Karfin Abota Da Dangantakar Al’adu

Baje Kolin Nuna Hotuna Tsakanin Sin Da Afrika Na Zurfafa Karfin Abota Da Dangantakar Al’adu

November 13, 2026
Tinubu Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Murƙushe ’Yan Daba Gabanin Zaɓen 2027

Tinubu Ya Umarci Jami’an Tsaro Su Murƙushe ’Yan Daba Gabanin Zaɓen 2027

November 13, 2026
An Yi Taro Na Farko Na Kwamitin Hadin Gwiwa Na Sin Da Afrika Kan Kimiyya Da Fasaha

An Yi Taro Na Farko Na Kwamitin Hadin Gwiwa Na Sin Da Afrika Kan Kimiyya Da Fasaha

November 13, 2026
Kuzarin Da Ke Raya Dangantakar Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Karuwa

Kuzarin Da Ke Raya Dangantakar Sin Da Amurka Na Ci Gaba Da Karuwa

November 13, 2026
Han Zheng Ya Halarci Babban Taron Sinanci Na Duniya Na Shekarar 2026

Han Zheng Ya Halarci Babban Taron Sinanci Na Duniya Na Shekarar 2026

November 13, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.