Gwanatin Jihar Yobe ta raba kayan abinci ga magidanta 137,000 a don rage radadin cire tallafin man fetur.
Dokta Muhammad Goje, Sakataren zartarwa na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na Jihar, ya shaida wa taron manema labarai a jihar a ranar Laraba cewa, an raba shinkafa, masara, taliya da kuma kayan abinci ga magidanta da suka amfana da rabon.
- Bayan Tsawon Shekaru: Hada-Hadar Shanu Da Rakuma Ta Farfado A Jihar Yobe
- Jihar Yobe A Shekara 32 Da Kafuwa: Ci Gaba Da Koma-bayanta
Goje ya bayyana cewa an raba kayayyakin ne ga wadanda suka ci gajiyar tallafin a kananan hukumomin Damaturu, Fine, Potiskum, Bade, Geidam da Jakusko.
Goje ya ce kowane magidanci ya samu tsakanin 20kg zuwa 50kg na hatsi.
“Kashi 69 cikin 100 na wadanda suka amfana sun samu kayan a matakin daidaiku yayin da sauran kashi 31 cikin 100 suka samu nasu ta hanyar yin rakuni ko hadaka,” in ji shi.
Goje ya kara da cewa, an tantance wadanda suka ci gajiyar tallafin ta hanyar rajista da shawarwarin shugabannin sarakunan gargajiya da wuraren ibada, jam’iyyun siyasa, da gidajen marayu da na nakasassu da dai sauransu.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa sauran masu karamin karfi a sauran kananan hukumomi 11 na jihar za su ci gajiyar kayayyakin nan ba da jimawa ba.