Babu wani sauran sabon labari na kai hare-haren ‘yan kungiyar Boko Haram a gonakin manoma da dama a a Jihar Yobe, wanda sakamakon hare-haren ‘yan ta’addar a baya ya haifar da samun karancin abinci a jihohin da ke shiyyar Arewa Maso Gabashin wannan kasa.
Amma a ‘yan kwanakin baya, ayyukan kasuwancin dabbobi sun fara dawowa ka’in da na’in, inda ‘yan kasuwa daga sassa daban-daban na kasar nan ke zuwa Jihar Yobe domin sayen kayan abinci da kuma dabbobi.
- Jami’an NSCDC Sun Cafke Matashin Da Ya Sace Babur Din Abokin Mahaifinsa
- NNPP Na Zargin Kwankwaso Da Hannu Wajen Nasarar Gawuna Da Kwace Zaben Kano A Kotu
Wasu daga cikin ‘yan kasuwa a Kananan Hukumomin Potiskum, Geidam da kuma Damaturu a jihar sun tabbatar da cewa, duk da kalubalen rashin tsaro da jihar ta fuskanta a baya da kuma wasu sassan jihar, amma a yanzu kasauwancin dabbobin ta dawo.
Daya daga cikin ‘yan kasuwa kuma Sarkin Turakin Potiskum, Lamido Damina Yarima ya bayyana cewa, kafin hare-haren ‘yan Boko Haram, sama da motar tirela 50 a duk mako ke zuwa kasuwar shanu ta Potiskum, domin kwasar shanu zuwa wasu sassan Nijeriya, wanda a yanzu haka duk mako ake jigilar dabbobi a kasuwar kasa da guda 40. Ya ce, a yanzu ana zuwa kasuwar jihar ana sayen dabbobi da sauran kayan amfanin gona a duk mako.
Shi ma a nasa jawabin, Shugaban Kungiyar Mahauta na Potiskum Alhaji Ibrahim Yunusa Mali ya bayyana da cewa, a 2005 zuwa 2008, sama da Shanu 50 zuwa 80 mahauta suke yankawa a Potiskum, amma yanzu kasa da 20 kacal ake iya yankawa a kullum.
Ya ce, amma yanzu da ayyukan ‘yan kugiyar Boko Haram suka kawo karshe, hada-hadar kasuwanci ta dawo ganin cewa, jama’a na ci gaba da yin kasuwancinsu.
Kazalika, wani mai sayar da dabbobi a kasuwar Mallam Bana Aramma, ya sanar da cewa hada-hadar kasuwanci na kara ci gaba tare da habaka a kasuwar ganin yadda ayyukan ‘yan Boko Haram din suka zama tarihi.
Shi ma Saleh Damniya Gamdu, Maino da Jakana sun ce, sama da Tirala 50 na shanu ake jigilar daga kasuwar Kura-Reta da ke Jihar ta Yobe.