Mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar nan na Arewacin Nijeriya, Dauda Kahutu Rarara ta kubuta daga hannun ‘yan bindigar da suka sace ta.
Idan ba a manta ba an sace mahaifiyar mawakin, Hauwa’u Adamu a ranar 28 ga watan Yuni, 2024 a kauyen Kahutu da ke karamar hukumar Danja a Jihar Katsina.
- Abba Ya Sake Nada Tsohon Sarkin Gaya Da Wasu Sabbin Sarakuna A Kano
- Zargin Karkatar Da Biliyan 2.8: Gwamnatin Kano Ta Maka Sule Garo Da ‘Yan Uwansa Biyu A Kotu
Sai dai bayan sace tsohuwar mai shekaru 75 a duniya, jami’an ‘yansanda a jihar suka baza koma, inda suka cafke mutum biyu da suke zargi da hannu a sace ta.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya ce an sace mahaifiyar mawakin da misalin karfe 1:30 na dare.
Ya zuwa yanzu dai an tabbatar da kubutar mahaifiyar mawakin, amma babu cikakken bayani ko an biya kudin fansa kafin sakinta.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp