Mahaifiyar tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya, Rt Hon Yakubu Dogara, Mama Saratu Yakubu Tukur ta kwanta dama tana da shekara 103 a duniya.
A wata sanarwar da Dogara ya fitar mai dauke da sanya hannunsa a madadin iyalan mamaciyar a daren ranar Juma’a, ya ce, za a sanar da lokacin biso da mata bikin bankwana lokacin da ya dace.
NPA Ta Bankado Masu Yi Wa Shirinta Na Rage Cunkoson Motoci A Apapa Zagon Kasa
Yawan Sinawan Da Suka Rasu Sakamakon Girgizar Kasa Ya Karu Zuwa 148
Dogara wanda shine autan mamaciyar ya ce, “Muna masu kankantar da kai ga mika wuya ga ikon Allah inda muke sanar da rasa mahaifiyarmu, kaka, Mama Saratu Yakubu Tukur a ranar Juma’a 22 ga watan Disamban 2023 tana da shekara 103 a duniya.”
Sanarwar ta ce, tabbas sun shaidi marigayiyar ta yi rayuwa mai ban sha’awa da kokari wajen hidimtawa, sadaukar da kai gami da hidima wa jama’a da bauta wa Allah.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp