Wasu mutum 19 daga Jihar Kano sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota a yankin Kwanar Maciji da ke Ƙaramar Hukumar Pankshin, a Jihar Filato.
Shugaban Ƙaramar Hukumar, John Dasar, ya bayyana cewa motar ta kama da wuta ne yayin da mutanen ke kan hanyar komawa gida daga ɗaurin aure da aka yi a Ƙaramar Hukumar Barikin Ladi ranar Asabar.
- Majalisa Ta Tuhumi JAMB Kan Kashe Biliyan 2 Kan Abinci Da Maganin Sauro
- Huldar Sin Da Afirka Za Ta Zama Abin Koyi Wajen Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Daukacin Bil’adama
A cewarsa, an ceto mutum 11 ciki har da direban motar da wasu fasinjoji, amma sun ji munanan raunuka.
Sauran fasinjoji 19 sun ƙone ƙurmus har ba a iya gane su.
An garzaya da waɗanda suka tsira da ransu zuwa Babban Asibitin Pankshin, inda ake ba su kulawar gaggawa.