‘Yan bindiga sun kashe wasu mutane takwas a lokacin da suka kai wani hari kan ayarin motocin ‘yan kasuwa da ke dawowa daga kasuwar garin Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Wata majiya mai tushe, wanda shugaban kungiyar direbobi a yankin, Kabiru Dangaye, ya bayyana cewa ‘yan ta’addar sun bude wuta kan ‘yan kasuwar ne a daidai lokacin da sojoji dauke da makamai suka yi wa ‘yan kasuwar rakiya cikin motoci 25 a ranar Juma’a.
- Kisan Katsina: Mun Rasa Rayuka 102 -Shugaban Al’umma
- Gwamnatin Nijeriya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Da Aka Yi Wa ‘Yan Banga A Katsina
Ya ce mutane takwas ne suka mutu nan take sakamakon harin yayin da aka kai wadanda suka jikkata asibiti don kula da lafiyarsu.
Shugaban ya ce, “Direban mu sun jira sa’o’i da dama kamar yadda suka saba kafin sauran direbobi da ‘yan kasuwa su zo daga unguwannin makwabta domin fara tafiya. Muna da motoci kusan 25 daga nan sai muka kira sojoji su zo su yi mana rakiya kamar yadda muka saba, sojoji suka shiga motarsu.”
Dangaye ya kara da cewa, sun tashi daga Mai Dabino da ke yankin Danmusa, inda suka tashi a cikin ayari, inda suka wuce Sabon Garin Nasarawa da Mahuta, sai suka yi kwanton bauna a kewayen unguwar Makera.
“’Yan ta’addar sun kasu kashi hudu ne kuma a lokacin da babbar motar ta isa rukuni na uku ne ‘yan ta’addar suka fara harbin. A lokacin da sojoji suke tuki a baya, da nufin tafiya gaba da sauri, sai wasu ‘yan ta’addar suka fara harbe-harbe a kansu, amma sojoji sun yi ta harbin kan mai uwa da wabi, saboda karfinsu, ‘yan ta’addar sun yi galaba a kan sojoji.” a cewarsu.
Dangaye ya kara da cewa an yi kira don a kawo dauki ga tawagar da karin sojoji domin taimakawa ‘yan kasuwar.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ba ta ce uffan ba kan harin, duk da kokarin jin ta bakin mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Abubakar Sadik, ya ci tura har zuwa lokacin mika rahoton.