Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe ‘yan sintiri tara a dajin Burra a karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi.Â
An ruwaito cewa, ‘yan bindigar sun kashe ‘yan sintirin ne a yayin suka bi sawun ‘yan bindigar a maboyarsu a dajin na Burra.
- Tinubu Ya Nada Musa Aliyu A Matsayin Shugaban ICPC
- ‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da ‘Ya’Ya 2 Na Dan Majalisar Dokokin Jihar Kwara
Kazalika, a ranar Litinin Yahaya Shuaibu Jami’n hulda da jama’a na daya daga cikin kungiyoyin ‘yan sintirin da aka hallaka da ake yi wa kungiyar lakabi da kungiyar ‘yan sintiri ta ‘Yan Ba Beli’, ya tabbatar da kashe ‘yan sintirin tara.
Sai dai, Yahaya ya ce, daga cikin wadanda aka kashe, mutum daya ne ba dan kungiyarsu ba.
Bugu da kari, ya ce sun saba gudanar da yin aikin na sintirin ne a tare don fatattakar ‘yan bindigar daga cikin dajin wanda ya ce, shafe mako suna gudanar da aikin.
A cewarsa, an kashe su ne da maraicen makon da ya wuce, inda ya kara da cewa, bisa bayanan da suka samu, ‘yan sintirin sun samu nasarar cafke wasu daga cikin ‘yan bindigar a maboyarsu a kauyen Gamji kafin daga baya, ‘yan bindigar su bude masu wuta.
Bugu da kari, ya bayyana cewa, ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro na farin kaya a wajen shigen duba ababen hawa a karamar hukumar Ningi.
Sai dai, mai magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar, bai fitar da wata sanarwa akan lamarin ba.