Akalla daliban firamare da sakandare 200 aka yi garkuwa da su a kauyen Kuriga da ke Karamar Hukumar Chikun a jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a lokacin da daliban ke taron asambili da misalin karfe 8:30 na safe.
- ‘Yan Bindiga Sun Kashe Makiyayi Da Shanu 35 A Wani Sabon Harin A Filato
- Sudan Ce Kasa Mafi Fama Da Yunwa A Afrika – MDD
Yaran da lamarin ya rutsa da su, kamar yadda wani ya tabbatar wa kafar yada labarai ta BBC, suna tsakanin shekarun 15 zuwa 18.
Ko a watan Janairun wannan shekara wasu ‘yan bindiga sun shiga kauyen Kuriga, inda suka kashe shugaban makarantar tare da yin garkuwa da matarsa.
Kuriga wani kauye ne da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, yankin da ya yi kaurin suna wajen ayyukan ‘yan bindiga.