Kasar Sin ta ce ba za ta taba tilastawa kasashen duniya koyi da dabaru ko manufinta na raya kasa ba, haka kuma ba za ta amince wata kasa ta kakaba mata nata tsari ba.
Hakika, kasar Sin ta riga ta zabi hanyarta ta raya kasa da tabbatar da tsaro da tafiyar da harkokinta na cikin gida tare kulawa da al’ummarta. Ta yi, kuma an ga irin nasarori da dimbin ci gaba da ta samu.
Kasashe da yankuna sun bambanta, haka ma al’adu da tsaruka, kuma a tunanina, wannan shi ya sa duniyar ta zama abun sha’awa. Don haka, kamata ya yi bambancin dake tsakaninmu, ya zama hanya ta samu karin ilimi da wadata, ba wai ta nuna wariya ko danniya ba.
Kamar yadda Hausawa kan ce, mai daki, shi ya san inda yake masa yoyo, gwamnati da al’umma ne suka san karfi da arzikin da kuma rauninsu, haka kuma su ne suka san yanayi da al’adun da bukatunsu, don haka, bai dace a ce wata kasa daga waje ce za ta tsara musu dabarun raya kansu ba.
Kamar yadda mataimkain shugaban sashen wayar da kai na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Sun Yeli ya bayyana, a shirye kasar Sin take ta ba kasashen duniya damar koyon dabarunta idan suna sha’awa, amma ba bisa tilas ba.
Ina ganin, yanzu kai ya riga ya waye, kasashe sun san tsarin da ya dace da su da kuma wadanda ba su dace, haka kuma sun san mai kaunarsu da gaske. Haka kuma kowa a duniya shaida ne na yadda kasar Sin ta gina kanta da karfin da tsari da dabarun da ta zabarwa kanta ba tare da danniya ko mulkin mallaka ko kwaikwayon wani ba.
Lokaci ya yi da ya kamata kasashen duniya su yi yaki da kokarin da kasashe masu ganin suna da karfi ke yi, na kakaba musu irin na su tsari ko yi musu danniya.
Dole ne shugabannin kasashe musammam na Afrika, su rika la’akari da yanayin da suke ciki da kuma bukatun al’ummominsu domin tsara manufofin da zai dace da su tare da ba su ikon tsaya da karfarsu ba zama ‘yan amshin shata ba.