Ana fargabar wata mai yi wa kasa hidima da wata mata mai juna biyu tare da wasu fasinjoji biyar sun mutu a wani hatsarin kwale-kwale a Bayelsa.
Hatsarin ya afku ne da yammacin ranar Asabar a tsakanin Otuan da Ayama da ke Karamar Hukumar Ijaw ta Kudancin jihar.
- Farashin Gas Din Girki Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi — NBS
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Hakimi Da Dansa A Bauchi
Rahotanni sun ce kwale-kwalen mai daukar fasinjoji 15 ya kife, inda ya nutse a yayin da yake tunkarar Ayama zuwa bakin ruwa, a daidai lokacin da ake tafka ruwan sama.
Haka kuma cikin wadanda abin ya shafa har da wata uwa tare da ‘ya’yanta guda biyu da wani basaraken Otuan mai shekaru 70 kuma mahaifin wani dan jarida a jihar, Cif Lucky Daniels.
Daily Trust ta rawaito cewa har yanzu ba a ga wadanda abin ya rutsa da su har yanzu ba a gansu ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto yayin da masu ruwa da tsaki a yankin ke aikin neman ceto su a gabar tekun unguwar Ayama.
Shugaban kungiyar ma’aikatan ruwa a Otuan, Joseph Shedrack, ya bayyana cewa matukin kwale-kwalen mai suna Lucky Christopher, wanda ya tsallake rijiya da baya, ‘yan sanda sun tsare shi bisa zargin tukin ganganci.
Shugaban kungiyar Maritime na jihar, Ipigansi Ogoniba, ya ce har yanzu ba a ga mutane shida ba.
Jami’in hulda da jama’a na NYSC a jihar, Mathew Ngobua, bai amsa kiran sa ba kuma har yanzu bai dawo da sakon wayar da aike masa ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce har yanzu suna jiran karin bayani domin gano ko su waye.