Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya amsa tambayar da aka yi masa a yau Lahadi, game da yada zangon da mataimakin jagoran yankin Taiwan Lai Ching-te ya yi a kasar Amurka, yana mai cewa, kasar Sin na adawa da duk wata mu’amala a hukunce, da ake yi ta kowace hanya tsakanin Amurka da Taiwan, kana, tana adawa da duk wata ziyarar da masu yunkurin balle yankin Taiwan daga kasar Sin suka yi a Amurka, bisa ko wane irin dalili ko hujja, sa’annan tana matukar adawa da duk wata tuntubar juna, da aka yi ta kowace hanya, tsakanin gwamnatin Amurka da mahukuntan Taiwan. Kakakin ya ce, Sin tana jin matukar takaici, gami da yin tir da danyen aikin da Amurka ta yi, na samar wa Lai Ching-te damar yada zango a kasar.
Kakakin ya kara da cewa, Amurka ta samar wa Lai Ching-te damar gudanar da harkokin siyasa a Amurka, bisa hujjar yada zangon da ya yi a kasar, al’amarin da ya sabawa muhimmiyar manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, da kawo babbar illa ga ikon mulki, da cikakken yankin kasar Sin.
Haka zalika, abubuwan da suka auku sun sake shaida cewa, babban dalilin da ya jawo zaman doya da manja a mashigin tekun Taiwan shi ne, yunkurin da mahukuntan Taiwan suke yi na neman samun ‘yancin yankin, ta hanyar dogaro da Amurka, gami da yunkurin da Amurka ta yi, na kawo tsaiko ga ci gaban kasar Sin bisa batun Taiwan.
Rahotanni na cewa, a ranar 12 ga watan Agusta, Lai Ching-te ya kama hanya zuwa kasar Paraguay, don halartar bikin rantsar da shugaban kasar, amma kafin nan ya fara “yada zango” a kasar Amurka. (Murtala Zhang)