Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a jiya 24 ga wata cewa, daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Agusta, an gudanar da taron koli na BRICS karo na 15 a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron.
A yayin taron, shugaba Xi Jinping da sauran shugabannin kasashen BRICS sun amince da gayyatar kasashen Saudiyya, da Masar, da Hadaddiyar Daular Larabawa, da Argentina, da Iran da kuma Habasha, don su zama mambobin BRICS. Kasar Sin na taya wadannan kasashe murna!
Jami’in ya ce, aiki din na fadada mambobin BRICS na da ma’ana a tarihi. A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta karbi bakuncin taron shugabannin kungiyar ta BRICS, kuma ta fara aikin fadada mambobin kungiyar. Tun daga wannan lokacin, kasar Sin take kokari tare da sauran mambobin kungiyar BRICS don ci gaba da inganta aikin.
Sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da ma kasashe masu tasowa da yawa suna la’akari da shiga kungiyar BRICS, kuma kasashe fiye da 20 ne suka gabatar da bukatunsu na shiga kungiyar, wanda ke nuna yadda kungiyar BRICS take jawo hankulan sauran kasashe masu tasowa, da kuma yadda kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da kasashe masu tasowa suke nuna sha’awa da fatansu matuka wajen kara gudanar da hadin gwiwa tsakaninsu.
Wannan matakin na fadada BRICS ya nuna aniyar kungiyar kasashen BRICS na hada kai da sauran kasashe masu tasowa, wanda ya dace da fatan al’ummomin duniya, da moriyar bai daya ta sabbin kasashen da tattalin arzikinsu ke bunkasa da ma sauran kasashe masu tasowa. Har ila yau, ya kasance wani mafari na hadin gwiwar kasashen BRICS, wanda zai sanya sabbin kuzari a cikin tsarin hadin gwiwar BRICS, da kara karfin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duniya gaba daya. (Mai fassara: Bilkisu Xin)