Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin a gaggauta sakin matashin da ‘yansanda ke tsare da shi bisa zargin cin mutuncinsa a shafukan sada zumunta.
Mahaifin matashin, Malam Garba Isa, ya shaida wa manema labarai cewa, a ranar 11 ga watan Disamba, 2022, ‘yansanda suka kama dansa bisa zargin zagin gwamnan a shafukan sada zumunta, ya kuma yi kira ga hukumomi da su duba yiwuwar sakin dansa.
- Mata Za Su Yi Wa PDP Ruwan Kuri’a A Sakkwato – Farfesa A’isha Madawaki
- Argentina Ta Ayyana Yau A Matsayin Hutu Don Murnar Lashe Kofin Duniya
Wata sanarwa da babban daraktan yada labaran gwamnan, ya raba wa manema labarai, Mamman Mohammed, a ranar Talata, ya ce gwamnan ba shi da masaniya game da kama shi tare da tsare shi, ya ce ba lallai ba ne a kamo wani da ya zage shi ko kuma sukar shi.
“Wannan shi ne shugabanci kuma muna sane da shi, don haka, ba zan iya ba da umarnin tsare kowa b.
“Har sai da wani ya ja hankalina game da lamarin, ban san an kama shi ba, yanzu na ba da umarnin a gaggauta sakinsa.
“Amma yana da kyau a lura cewa duk da cewa gwamnatin Buni mai sassauci ce, amma ya kamata guje wa suka mara ma’ana.”
Mohammed ya ce “An kuma tunatar da masu amfani da shafukan sada zumunta da su kasance masu natsuwa da kuma daukar nauyin mutunta hakkin kowa da kowa, jam’iyyun siyasa, bambancin addini da al’adu musamman yadda ake ci gaba da yakin neman zabe.”