A ranar Laraba ce, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kasafin kudi na naira tiriliyan 27.5 ga gamayyar majalisun dokoki na tarayya a wani zaman a hadin gwiwa da suka yi a majalisar wakilai.
Sai dai kuma majalisun kasar suna fuskantar kalubale na amincewa da kasafin kudin kafin karshen watan Disamba.
- An Haramta Shan Sigari A Wuraren Shakatawa Da Makarantu A Faransa
- Ministan Wajen Sin Ya Jaddada Shawarar Kafa Kasashe 2 A Matsayin Hanyar Warware Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
Majalisar zartarwa ta amince da kudirin kasafin kudin a wurin taronta, kamar yadda ministan kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Atiku Bagudu ya shaida wa manema labarai na fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Ya ce ana tsammanin samun kudaden shiga da suka kai na naira tiriliyan 18.32.
A cewarsa kudirin na naira tiriliyan 27.5 ya karu da sama da naira tiriliyan 1.5 idan aka kwatanta da kasafin yi na bara na naira tiriliyan 26.01.
Ya kuma ce gibin kasafin kudin ya yi kasa idan aka kwatanta da na bana.
‘Yan majalisar za su yi aiki ba dare ba rana don tantance alkaluman tare da zartar da kudurin doka wajen cika burin shugaban kasa da yake sa ran fara amfani da kasafin tun daga ranar 31 ga Disamba.
Wannan ya yi daidai da manufar tsarin kasafin kudi daga watan Janairu zuwa Disamba.
Wata majiya ta ce: “Kar ku manta cewa shugaban majalisar dattawa ya sha alwashin cewa majalisar ta 10 za ta ci gaba da gudanar da tsarin kasafin kudi na watan Janairu zuwa Disamba.
“Har ila yau, kar ku manta cewa shugaban kasa ya gargadi ministoci da shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su rika girmama kiran kwamitocin majalisar dokokin kasa a ko da yaushe.
“Lokaci ya wuce da shugabannin ma’aikatun gwamnati za su fice daga kasa don guje wa gurfana a gaban kwamitocin majalisu.
“Bayan gabatar da kasafin kudin a ranar Laraba, majalisun kasa suna da wa’adin wata daya kacal wajen tantance kasafin tare da amincewa da shi.”
Wata majiyar kuma ta ce shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar dattawa, Solomon Adeola ya nuna cewa zai yi wahala majalisa ta iya gudanar da wannan aiki a kan lokaci.
Majiyar ta ci gaba da cewa: “Lokacin da yake shugabancin kwamitin kudi a majalisar dattawa ta 9, ya tabbatar da cewa an amince da wasu muhimman kudirori kamar na kudade a lokacin da ya dace duk da ya yi aiki na sa’o’i 24 kafin a kammala aikin.
“Ya ce ko ma a ce shugabannin ma’aikatu su bayyana a gaban kwamitocin majalisa wajen kare kasafinsu zai dauki lokaci.”