Majalisar Dattawa ta amince da sabuwar doka da ta tanadi ɗaurin rai da rai ga duk wanda aka samu da laifin lalata da yaro ko yarinya ƙarama.
Dokar na son kare ƙananan yara, ta shafi maza da mata baki ɗaya, ba tare da wani zaɓi na biyan tara ba.
- Jami’an Kasashen Afrika Na Koyon Dabarar Yaki Da Talauci Ta Sin A Jihar Ningxia
- Gwamna Yusuf Ya Buƙaci Hukumar NBC Da Ta Sa Ido Kan Gidajen Rediyo Da Talabijin Na Yanar Gizo
Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa), ya ce yara ba su da iko ko yardar wajen amincewa da yin jima’i kuma irin wannan abu na jefa su cikin tashin hankali har abada.
Da farko ya ba da shawarar a ɗaure mai laifi na tsawon shekaru 20, amma yawancin sanatoci sun nemi hukunci mafi tsauri.
Sanata Muhammad Adamu Aliero (Kebbi ta Tsakiya) ya bayar da shawarar ɗaurin rai da rai, kuma majalisar ta amince da wannan gyara gaba ɗaya.
Dokar za ta tafi Majalisar Wakilai don amincewa kafin a aike wa Shugaban Ƙasa domin sanya hannu.