Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin dokar da ke neman bai wa jami’an Hukumar Kiyaye Haɗurra (FRSC) damar ɗaukar makamai, a matakin karatu na biyu.
Wakilan da suka ɗauki nauyin wannan ƙudiri su ne Abiodun Derin Adesida da Olaide Lateef Muhammed. Ƙudirin na neman gyara dokar FRSC na shekarar 2007 don samar da wata rundunar musamman mai ɗauke da makamai a hukumar.
- Kashin Shettima Ya Dawo Nijeriya Bayan Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Na 79
- Tallafin Ambaliya: Ɗan Majalisa Ya Buƙaci Gwamnatin Sakkwato Ta Bayyana Yadda Ta Kashe Biliyan Uku
Har ila yau, dokar ta tanadi ba da fa’idodi ga jami’an hukumar da suka kai matsayin mataimakin Kwamanda, wanda ya haɗa da fansho da sauran alawus-alawus bayan ritaya. Hakan zai kuma bai wa FRSC cikakken iko a kan kula da harkokin zirga-zirga, da tsare-tsaren lafiya a tituna, da kuma tabbatar da doka domin rage haɗurra, kwashe duk wani abu da ka iya kawo cikas a kan hanyoyi, da wayar da kan jama’a kan kiyaye dokokin hanya.
Bugu da ƙari, an amince da wani ƙudiri wanda ya buƙaci hukumar FRSC ta ƙara amfani da fasahar zamani a ayyukanta, irin su tsarin sarrafa zirga-zirga ta kai tsaye da nazarin bayanai don inganta tsaron hanyoyi da rage karya dokokin hanya.
Kwamitin majalisar mai kula da FRSC zai ci gaba da duba wannan ƙudiri.