Majalisar Dattawa ta amince da wani kudiri na gyara dokar mafi karancin albashi na kasa na 2019, inda ta amince da karin albashi daga Naira 30,000 zuwa Naira 70,000.
Kudirin ya kuma rage lokacin sake duba mafi karancin albashi daga kowace shekara biyar zuwa shekara uku.
- Kyari Ya Musanta Zargin Dangote Na Wasu Ma’aikatan NNPC Na Hada-hadar Mai A Malta
- Tinubu Ya Aike Wa Majalisa Sabon Mafi Ƙarancin Albashi Don Tantancewa
Kudirin dokar da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar, ta tsallake karatu na farko da na biyu a zaman majalisar na ranar Talata, wanda ta amince da shi.
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa kudurin dokar ya shafi bukatun kungiyoyin kwadago na baya-bayan nan na kara albashi saboda yanayin tattalin arzikin da ake ciki.
Bayan tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Kungiyar Kwadago, an kara mafi karancin albashi zuwa Naira 70,000.