Majalisar wakilai ta tsoma baki cikin batun zargin da hukumar shirya jarabawar share fagen shiga jami’a (JAMB) ta yi wa wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme na kirkirar sakamakon bogi wanda hukumar ta shirya na 2023.
‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar jarabawar ta gaza nuna dattaku kan lamarin da ya shafi karamar yarinya ta hanyar janye sakamakon jarabawarta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.
- Jami’ai Daga Sassan Kasa Da Kasa Sun Jinjinawa Manufar Gina Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ga Dukkanin Bil Adama
- Jami’ar Jihar Taraba Ta Rage Kudin Makaranta Da Kashi 50 Bisa Dari
Sun ce yana yiwuwa akwai hannun wani a cikin lamarin.
Daga nan ne majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da neman hukumar JAMB da ta dakatar da zartar da hukunci har sai majalisar ta kammala bincikenta.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar ta JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar ta bana.