Kwana guda da sanarwar da zabin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi masa, Majalisar Dattawa, ta tantance tare da tabbatar da nadin tsohon Sufeto Janar na ‘yansanda, Mista Solomon Arase (Mai ritaya) a matsayin sabon shugaban hukumar kula da harkokin ‘yansanda (PSC).
A jiya ne Majalisar ta amince da Arase bayan tsallake tantancewar kwamitin Majalisar Dattawa kan harkokin ‘yansanda da ke karkashin jagorancin Sanata Halluru Dauda Jika (Sanatan Bauchi ta tsakiya).
A lokacin da yake gabatar da rahoton aikin kwamitinsa a gaban Majalisar, Sanata Jika ya shaida cewar Arase ya cancanta ya kuma dace domin ya yi kokari sosai a lokacin da suke masa tambayoyi a yayin tantance shi, kana ya kuma tabbatar na da nagartar da zai iya jagorantar hukumar.
Bayan gabatar da rahoton, gaba daya Majalisar ta amince da tsohon IGP din da ya zama cikakken shugaban hukumar kula da harkokin ‘yansandan Nijeriya.
Buhari ta cikin wasikar da ya aike wa Majalisar Dattawan a ranar Talata, da shugaban majalisar, Sanata Ahmad Lawan ya karanta a gaban kwaryar Majalisar, ya bukaci Majalisar da ta yi la’akari da zabin da ya yi wa Arase tare da tantance shi domin ya zama shugaban hukumar.
Buhari ya ce nadin an yi a karkashin sashi 154 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.