Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin mai shari’a Kudirat Kekere Ekun a a matsayin alkalin alkalan Nijeriya.
Kudirat Kekere Ekun ta kasance alkalin alkalan Nijeriya ta riko tun a daga watan Agusta 2024 bayan da mai shari’a Olukayode Ariwoola ya yi ritaya daga matsayin.
- CMG Ya Gabatar Da Bikin Baje Shirin Bidiyo A Moscow Albarkacin Bikin Cika Shekaru 75 Da Kafuwar Janhuriyar Jama’ar Sin
- Ina Dalilin Da Ya Sa Amurka Ke Shirin Daina Amfani Da Manhaja Da Injuna Kirar Sin A Motoci Masu Kama Intanet?
An tabbatar da ita kan wannan matsayi ya biyo bayan bukatar da shugaba Bola Tinubu bayan ya aik ewa majalisar wadda shugabanta Godswill Alpabio ya karanta.
Tinubu ya ce ya mika bukatar kamar yadda sashe na 231 (1) na kundin tsarin mulkin Nijeriya wanda aka yi wa gyara ya ba shi ikon nada alkalin alkalai bayan karbar shawara daga hukumar kula da alkalai ta kasa.
Bayan tambayoyi da kuma tantancewa a karshe majalisar datttawa ta tabbatar da nadin Kekere-Ekun a matsayin alkalin alkalan Nijeriya.
A lokacin da ta ke bayani gaban majalisar tabbatar da ita, ta ce za ta rungumi aiki da fasahar zamani a ayyukan shari’a a Nijeriya.
Alkalan kotun koli da na daukaka kara na cikin wadanda suka raka ta majalisar dattawa domin tantance ta a ranar Laraba.