A ranar Litinin ne Majalisar Dattawa ta tantance Dakta Mariya Mairiga Mahmud wacce ta Maye Gurbin Maryam Shetty a matsayin minista daga jihar Kano.
Dakta Mariya, ta maye gurbin sunan Maryam Shetty ce da shugaba Tinubu ya cire sunanta a satin da ya gabata.
Maryam Shetty ta isa Majalisar Dattawa tana jiran tantanceta, kwatsam sai labari ya iske ta cewa an sauya sunanta da wata tsohuwar kwamishiniyar ilimi lokacin gwamnatin Ganduje a Kano, Mariya Mahmud.
Sauyan sunan Shetty da Mairiga ya janyo ce-ce-ku-ce shafukan sada zumunta.