Matsalar gararanbar al’majirai da yaran da basa zuwa makaranta na ci gaba da kasancewa babban kalubalen dake haifar da abubuwa marasa dadi musanman a yankin Arewa masu Yammacin Nijeriya.
Dan Majalisar Wakilai daga Jihar Sokoto, Dakta Shehu Balarabe Kakale ne ya dauki nauyin wani kudirin doka da ya nemi kafa hukumar da za ta kula da ilimin tsangaya da yaran da ba sa zuwa makaranta ta yadda za a samar da kyakkyawan tsarin ilimi da zai magance matsalar jahilci, da samar da ayyukan yi ga matasa.
- An Fitar Da Rahoton Amurka Ta Keta Hakkin Dan Adam Na Makaurata Da Yan Gudun Hijira
- Gwamnati Ce Ta Yi Min Magudin Zabe Da Karfin Soji – Matawalle
Yanzu haka dai kudirin ya zartar karatu na biyu kuma ya samu gagarumin goyan baya daga masu ruwa da tsaki a tarn da Majalisar ta gudanar ranar talartan nan.
Da take bayanai a taron Shugabar Kungiyar Dake Fafutukar Inganta Rayuwar Al’ummar Najeriya Dakta Fatima Goni, wadda har ila yau na daya daga cikin wadanda suka ba da gagarumar gudunmawa a kokarin samar da dokar, ta ce dalilin da ya suka goyi bayan wannan doka shi ne kungiyarsu tana da ra’ayi na taimaka wa gajiyayyu musanman al’majirai.
Shugabar kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin mai magana da yawunta Hajiya Riskatu Abdulaziz.
”Tun da dadewa mu ma mun bukaci samar da irin wannan doka ta kafa hukumar, dalili da cewa kungiyarmu muna da son taimaka wa gajiyayyu musanman al’majirai shi ya sa muke farinci da marhabin da wannan abu”. In ji Dakta Fatima Goni
A daya bangaren kuma ma’aikatar ilimi ta tarayya bata goyi bayan kudirin dokar ba, a cewarta wai ba ta da isassun kudade, kudaden dake aljihunta za su Kara tsiyayewa”
Taron dai ya samu halartar masu ruwa da tsaki kan harkar ilimi da suka hada da jama’in gwamnati, da Malaman addini da kuma saraukunan gargajiya da sauransu.