Majalisar wakilai a ranar Talata, ta yi watsi da kudirin dokar yi wa kundin tsarin mulkin kasa gyaran fuska, da ke neman a rika Karɓa-karɓa a ofishin shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa a tsakanin shiyyoyi shida na siyasar Nijeriya.
Bugu da kari, majalisar ta yi watsi da wasu kudirorin sauya kundin tsarin mulkin kasar guda shida da aka jera a cikin takardar gabatar da sabbin kudirin domin tantancewa.
Sai dai, Majalisar ta yanke shawarar dawo da takardar kudirin a ranar Laraba domin sake la’akari da su a kan cancantar su ko akasin haka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp