A ranar Alhamis ne majalisar wakilai ta yi watsi da kudirin dokar da ke neman yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima na shekarar 1999 domin samar da wa’adi guda na tsawon shekaru shida ga ofisoshin shugaban kasa da gwamnonin jihohi da kuma shugabannin kananan hukumomi.
Kudurin ya kuma ba da shawarar a rika zagayawa da kujerun shugaban kasa da na gwamnoni zuwa shiyya (Arewa da kudu), da kuma gudanar da dukkan zabuka a rana daya.
- Gwamnan Bauchi Ya Gabatar Da Fiye Da Biliyan 465 A Matsayin Kasafin Kuɗin 2025
- Shugabannin Arewa Na Baya Sun Gaza – Uba Sani
Kudurin dokar da aka gabatar na neman sauya Sashe na 76, 116, 132, 136, da wasu sassan Kundin Tsarin Mulki na 1999 (kamar yadda aka gyara).
Kudirin ya kafa hanzarin cewa, “wadannan gyare-gyaren na da nufin dakile almubazzaranci da dukiya da ake yi duk bayan shekara hudu don gudanar da zabe da kuma daidaita tsarin gudanar da mulki.”
Sai dai a lokacin da kakakin majalisar, Hon. Abbas Tajudeen wanda ya jagoranci zaman majalisar ya nemi jin ra’ayin ‘yan majalisar kan kudurin, sun yi watsi da shi.