Sunayen Ministocin Tinubu Uku da majalisar dattawa taki tantance su a ranar Litinin din da ta gabata sabida rahoton tsaro da aka aike wa majalisar, Akwai yiwuwar dawo dasu majalisar don sake tantance su.
Wadanda lamarin ya shafa sun hada da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, Sanata Abubakar Danladi daga jihar Taraba, da tsohuwar shugabar bankin Nexim Stella Okotete.
Ministoci: Majalisar Dattijai Ba Ta Tabbatar Da Tantance Elrufai, Okotete Da Danladi Ba
Kakakin majalisar dattawa, Yemi Adaramodu ne ya bayyana hakan a ranar Talata, yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin na Channels inda ya ce, majalisar za ta sake gayyatar wadanda aka ki amince wa a tantance su idan majalisar ta gamsu da rahoton tsaro da za a aike mata nan gaba.
“Idan hukumar tsaro bata gamsu da su ba, Majalisa ma ba za ta iya amince musu ba. Don haka, sake gayyatar su ya danganta ne da rahoton hukumar tsaro da kuma ra’ayin shugaban kasa,” inji Adaramodu
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne Majalisar Dattawa ta amince tare da tabbatar da nadin ministoci 45 cikin 48 da Shugaba Bola Tinubu ya mika mata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp