Majalisar bayar da shawarwari kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC), ta kaddamar da taronta na shekara-shekara yau Talata, a nan birnin Beijing.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran shugabannin kasar ne suka halarci taron bude zaman na 3 na kwamitin CPPCC karo na 14 da ya gudana a babban dakin taron jama’a. (Fa’iza Mustapha)