Ofishin magatakardar majalisar tarayya ya fayyace iya matsayinsa kan rikicin da ya dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ya ce, ‘yan majalisar ne kadai ke da hurumin dawo da ‘yar majalisar da aka dakatar.
Babban magatakardar, a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja ta hannun Daraktan Yada Labarai, Mista Bullah Audu Bi-Allah, ya jaddada cewa ofishin yana gudanar da ayyukansa ne a matsayin hukumar gudanarwa ba tare da ikon sauyawa ko gyara hukuncin da Majalisar Dattawa ta yanke ba.
- Mujallar Qiushi Za Ta Wallafa Sharhin Xi Jinping Mai Taken “Zurfafa Dunkulewar Kasuwannin Kasa Ta Bai Daya”
- ‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Kan Masallata Tare Da Garkuwa Da Mutane A Zamfara
A cewar sanarwar, “Ofishin magatakarda ba shi da ikon yin bita, hanawa ko sauya hukuncin Majalisar Dattawa.”
Majalisar dattawa ta dakatar da Sanata Akpoti-Uduaghan a ranar 6 ga Maris, 2025, na tsawon watanni shida. Duk da cewa an kalubalanci lamarin a kotu, amma babbar kotun tarayya ba ta bayar da wani umarni na soke dakatarwar ba ko kuma tilasta sake dawo da ita bakin aiki.
A ranar 4 ga Satumba, 2025, Sanatar ta sanar da ofishin magatakarda akan aniyar ta na ci gaba da ayyukan majalisa, nan take, ofishin ya mika wasikar ga shugabannin majalisar dattawan.