Kwamitin majalisar dattawa na wucin gadi mai kula da satar mai a yankin Neja-Delta, ya ce ya fara bincike kan al’amuran da suka shafi satar mai da ayyukan nemo mafita kan satar a yankin Neja-Delta.
Shugaban kwamitin, Bassey Akpan ne ya bayyana hakan a lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a lokacin da suka isa filin jirgin sama na Fatakwal.
Akpan ya koka da yawaitar satar danyen man fetur da ake yi a Nijeriya, Inda ya alakanta lamarin da cewa abin takaici ne.
Ya ce kasar ta na asarar makudan kudaden da take samu, satar ta kawo cikas a samun adadin gangar mai da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta kayyade wa Nijeriya.
Ya ce, “Niyyarmu ita ce, mu ziyarci kowacce ma’ajiyar danyen Mai da ke yankin Neja-Delta don mu gani da idanmu, mu gano dalilin satar mai, da asarar da ake yi.”