Shugabancin Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya isa majalisar dattawa a yau Alhamis domin tantancewa a gaban kwamitin bai ɗaya na majalisar. An ce Amupitan ya isa zauren majalisar ne tare da gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Ododo, da wasu jami’ai na gwamnati.
Ana sa ran Sanatoci za su yi masa tambayoyi bayan ya gabatar da tarihin aikinsa da ƙwarewarsa kafin a yanke shawara kan amincewa da shi ko akasin haka.
Rahotanni sun bayyana cewa, da misalin ƙarfe 12:50pm na rana, Amupitan ya zauna a zauren majalisar dattawan bayan wakilin harkokin majalisar a fadar shugaban ƙasa, Sanata Abubakar Lado, ya jagorance shi zuwa ciki.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya tarɓi Amupitan da iyalinsa da sauran baƙi zuwa zauren majalisar kafin fara aikin tantancewar.
Tantancewar ta fara ne da misalin ƙarfe 12:55 na rana bayan shugaban majalisar ya yi jawabi kan tsarin da za a bi wajen gudanar da aikin.
Cikakkun bayanai za su biyo baya.