Majalisar Dattawa ta shelanta cewa, za ta gudanar da bincike kan yadda aka sayar da hannun jarin filayen tashi da saukar Jiragen sama na kasa da kasa na Malam Aminu Kano da kuma na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Majalisar wadda ta sanar da hakan a ranar Alhamis tana mai cewa, binciken ya zama wajibi domin ba a bi ka’ida ba kan yadda aka sayar da hannun jarin filayen Jiragen saman biyu.
- Akpabio Ya Nada Bamidele, Ndume, Umahi Da Asiru Manyan Mukamai A Majalisar Dattawa
- A Karon Farko Sanata Barau Ya Jagoranci Zaman Majalisar Dattawan Nijeriya
Majalisar ta dai cimma wannan matayar bayan wani kuduri da Sanata Kawu Sumaila, ya gabatar a zauren majalisar, inda Kawun ya bayyana cewa ba a bi dokar hukumar kula da Jiragen sama ta kasa (FAAN), da kuma ka’idar da ICRC ta tana ba wurin kulla yarjejeniyar filayen Jiragen saman biyu ba.
Ya ci gaba da cewa, bangaren zartarwa na gwamnatin tarayya a ranar 17 ga watan Mayu, ya amince da sayar da hannun jarin filin Jirgin saman Malam Aminu Kano har zuwa tsawon shekaru 30 ga kamfain Messrs na kasar Amurka.
Kawu ya ce, an yaudari bangaren zartarwa kan daukar wannan matakin don haka babu wani abu da ya fi dacewa, illa a soke wannan yarjeniyar baki-daya .
Kawun ya nuna damuwarsa kan yadda Nijeriya ke karbar kudin yarjejeniyar Dala Miliyan 1.5, alhali jimmalar kudin filin Jiragen saman Aminu Kano kadai ya kai dala miliyan 97.4.
Majalisar ta kuma yi tir da yadda aka kulla sayar da hanun jarin filayen Jiragen biyu.