Majalisar Dattawa za ta gudanar da zama na musamman a ranar Laraba, 24 ga Yuli, domin girmama tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13 ga Yuli yana da shekaru 82.
A cikin wannan zama, majalisar za ta yi nazari kan rawar da Buhari ya taka wajen bunƙasa ƙasa da kuma irin gadon da ya bari a tarihin siyasar Nijeriya.
- An Sanya Wa Titin Shendam Sunan Marigayi Muhammadu Buhari
- Ban Tsani Buhari Ba, Ina Sukar Sa Ne Kawai Kan Matsalar Tsaro – Ortom
Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta gudanar da irin wannan zama na girmamawa a ranar Alhamis da ta gabata, inda Shugaba Bola Tinubu ya yaba da salon shugabancinsa.
Marigayi Buhari, ɗan asalin Daura a Jihar Katsina, ya rasu a birnin Landan kuma an binne shi a garinsu ranar 15 ga Yuli, 2025, a wata jana’iza da manyan baki daga ciki da wajen ƙasa suka halarta. Yayi mulkin Nijeriya – daga 1983 zuwa 1985 a matsayin shugaban Soja, sannan daga 2015 zuwa 2023 a matsayin shugaban da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya.
A wani ɓangare na zaman majalisar ranar Talata, shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ya ƙaryata jita-jitar da ke yawo cewa an amince da ƙirƙirar sabbin jihohi, yana mai cewa har yanzu babu wani ƙudurin da ya kai matakin amincewa.