Majalisar dattijai, a ranar Alhamis, ta tabbatar da nadin alkalai 11 na kotun koli, bayan tantance su da kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin shari’a da kare hakkin bil’adama ya yi wanda Sanata Mohammed Monguno (APC – Borno ta Arewa) ya jagoranta.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen alkalan zauren majalisar bisa shawarar da majalisar shari’a ta kasa ta bayar, don cike guraben guraben Alkalam da suka yi ritaya daga aiki.
- Kotun Ƙoli Ta Kammala Sauraron Ƙarar Zaɓen Kano, Za Ta Sanar Da Ranar Yanke Hukunci
- Malamai A Kano Sun Gabatar Da Addu’o’i Kan Allah Ya Tabbatarwa Gawuna Nasararsa A Kotun Ƙoli
Alkalan kotun kolin da aka tabbatar sun hada da Mai shari’a Haruna Tsammani (Arewa-maso-gabas), wanda a baya ya jagoranci kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa, sai Mai shari’a Moore Adumein (Kudu-Kudu) da Mai Shari’a Jummai Sankey (Arewa Ta Tsakiya) da Mai Shari’a Chidiebere Uwa (Kudu-Gabas) da kuma Mai shari’a Chioma Nwosu-Iheme (Kudu-Gabas).
Sauran alkalan da aka nada sun hada da Justice Obande Ogbuinya (Kudu maso Gabas) da Mai Shari’a Stephen Adah (Arewa Ta Tsakiya) da Mai Shari’a Habeeb Abiru (Kudu maso Yamma), sai Mai Shari’a Jamilu Tukur (Arewa maso Yamma) da Mai Shari’a Abubakar Umar (Arewa-maso-Yamma), sai kuma Mai Shari’a Mohammed Idris (Arewa-maso-Yamma). Arewa-Tsakiya).
Daukaka darajar Alkalan zuwa kotun koli ya kawo adadin alkalan da ke kotun koli zuwa 21, wanda kamar yadda kundun tsarin mulkin 1999 ya tanada (wanda aka gyara).