Kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin iskar gas ya nemi ministan kudi Wale Edu, cikin mako guda ya yi bayani dalla-dalla kan yadda ya bayar da kwangila kuma ya amince da fitar da makudan kudade sama da Naira biliyan 100 ga kamfanonin da ke gudanar da ayyukan iskar gas da ke karkashin ofishin shugaban kasa (PCNG).
Bukatar ta zo ne a daidai lokacin da PCNG ke kokarin sake fitar da Naira biliyan 130 ga wasu kamfanoni da ba a tantance adadinsu ba, tare da yin biris da gargadin da kwamitin gas din ya yi tun farko na kashe kudade kan ayyukan samar da iskar gas ba tare da amincewar majalisar dokokin kasar ba.
- An Harbe Fitaccen Dan Bindigan Da Ya Addabi Mazauna Abuja A Sansaninsa
- Tsadar Rayuwa: Majalisar Wakilai Ta Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Lalubo Mafita
Tun da farko dai kwamitin ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu kan ayyukan CNG amma ya bukaci shugaban kasar da ya gaggauta gabatar da wani karin kasafin kudi ga majalisar dokokin kasar domin ci gaba da ayyukan iskar Gas.
Sai dai wasikar da ta bukaci ministan kudin da ya baiwa kwamitin cikakken bayani kan bayar da kwangilar da kuma fitar da sama da Naira biliyan 100, ta biyo bayan sabon koke ne da wata kungiyar da aka fi sani da “Good Governance and Transparency Front” ta gabatar, inda ta zargi shugaban kwamitin gudanarwar na Shirin Shugaban Kasa na CNG da amincewa da bayar da kudaden ba tare da bin ka’ida ba da kuma Dokar Bayar da Kayayyakin Jama’a, ta 2007.
Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da albarkatun iskar gas, Sanata Jarigbe Agom, ya bukaci ministan da ya mika wa kwamitin cikakkun bayanai na bayar da kwangila da kuma fitar da fiye da Naira biliyan 100 sannan kuma da jerin sunayen kamfanonin da aka baiwa kwangilar ayyukan