Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira ga gwamnatin mulkin Myanmar da ta saki Aung San Suu Kyi yayin da ya amince da kudurinsa na farko kan halin da ake ciki a yankin kudu maso gabashin Asiya mai fama da rikici.
Majalisar mai wakilai 15 ta shafe gwamman shekaru tana fama da rarrabuwar kawuna kan Myanmar kuma daga bayan nan ne ta cimma matsaya a kan rikicin kasar, wacce ke karkashin mulkin soja tun watan Fabrairun 2021, lokacin da aka hambarar da Suu Kyi.
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Sama Da 150 A Arewa Cikin Mako 2Â
- Zan Bayyana Dan Takarar Da Zan Mara Wa Baya A Janairu – Wike
Suu Kyi, mai shekaru 77, ta kasance a tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatinta kusan shekaru biyu da suka gabata tare da murkushe masu adawa da gwamnatin.
Kudirin da kwamitin ya cimma a ranar Laraba, ya bukaci gwamnatin sojin Myanmar ta saki wadanda take tsare da su, ciki har da Suu Kyi da tsohon shugaban kasar, Win Myint.
Ya kuma bukaci kawo karshen dukkannin nau’ikan rikici a kasar ba tare da bata lokaci ba, kana ya roki dukkannin bangarori su mutunta hakkin dan adam.
Amincewa da wannan kuduri, ya yi nuni da yanayi na kwarya-kwaryar hadin kai a cikin shekarar da rarrabuwar kawuna ta yi kamari sakamakon mamayar Ukraine da Rasha ta yi.