Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta tantance tare da amincewa da zabbabun Kwamishinoni 13 daga cikin 14 da gwamna Uba Sani ya aike mata.
Kakakin majalisar, Hon. Yusuf Dahiru Liman, a ranar Talata ya sanar da cewa majalisar ta amshi sunayen mutum 14 da gwamnan ke son su zama masa Kwamishinoni domin a tantance su.
Wadanda majalisar ta tabbatar da nadinsu a matsayin kwamishinonin jihar Kaduna akwai Hon. Aminu Abdullahi Shagali kakakin majalisar jihar na 8.
Sauran kuma sun hada da Umma Kaltume Ahmed, Mukhtar Ahmed, Arch. Dr.Ibrahim Hamza, Sule Shua’ibu, Shizzer Nasara Joy Bada, Professor Muhammad Sani Bello, Salisu Rabi, Professor Benjamin Kumari Gugong, Abubakar Bubba, Sadiq Mamman Lagos, Murtala Muhammad Dabo da kuma Patience Fakai.
Kazalika, daya daga cikin zababbun, Auwal Musa Shugaba, bai samu tantancewa da amincewar majalisar ba sakamakon gaza bayyana a kwaryar majalisar da bai yi ba.
Bayan kammala aikin tantancewar, shugaban kwamitin yada labarai na majalisar, Hon. Marah Henry Zachariah, ya ce, bisa kyawawan tarihi da zababbun suke da shi, za su tabbatar da yin ayyuka masu nagarta wajen sauke nauyin da ke kansu.