Majalisar Dokokin Kaduna ta rushe dokar da ta kafa hukumar kula da biranen Zariya da Kaduna da kuma Kafanchan.
A ranar Laraba Majalisar ta soke dokar da ta kafa hukumar wacce tsohuwar gwamnatin Nasir El-Rufai ta kirkiro a 2021.
- Sakataren Gwamnati Da Ministoci Na Ganawar Sirri Kan Zanga-zangar Matsin Rayuwa
- Yarjejeniyar Beijing: Mabudin Zaman Lafiya A Zirin Gaza
Majalisar ta ce ta soke dokar kula da biranen ne bayan hukuncin Kotun Koli na bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
“Don haka yanzu babu bukatar wannan hukumomi” da El-Rufai ya kafa a lokacinsa dake kula da biranen jihar.
Dama dai dangantaka ta yi tsami a tsakanin tsohon El-Rufai da majalisar dokokin jihar da kuma gwamnan yanzu, Uba Sani.
Zaman doya da manja tsakanin gwamnatin Uba Sani da El-Rufai har ta kai ga majalisar ta kafa kwamitin binciken Gwamnatin El-Rufai daga 2015 zuwa 2023.
Tsamin dangantakar tasu ta kai ga har El-Rufai ya maka Gwamnati da Majalisar dokokin Jihar bisa tuhumar da suka yi masa na kartatar da Naira biliyan 423.
El-Rufai, wanda ya bayyana zargin a matsayin “neman bata suna” ya maka majalisar dokokin a kotu domin neman hakkinsa.
Majalisar ta ce ta soke dokar kula da Biranen ne bayan hukuncin Kotun Koli na bai wa kananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu.
“Don haka yanzu babu bukatar wannan hukumomi” da El-Rufai ya kafa a lokacinsa da ke kula da biranen jihar.