A jiya ne majalisar dokokin jihar Zamfara ta zartar da wani kudiri domin samar da dokar hukunta masu aikata laifukan fashi da makami, satar shanu, kungiyoyin asiri, garkuwa da mutane, ta’addanci da sauran Laifuffuka.
Kakakin majalisar, Nasiru Magarya, ya ce amincewa da kudirin ya zama dole, tare da la’akari da kokarin Gwamna Matawalle na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.
Magarya Ya kuma yaba wa Gwamna Bello Matawalle bisa bullo da sabbin tsare-tsare da matakan dakile matsalar tsaro a jihar.
Majalisar kuma ta karanta wani sabon kudirin dokar kafa kwalejin koyon aikin jinya ta jihar Zamfara a Gusau, a karon farko.
Shugaban majalisar Alhaji Faruku Dosara ne ya gabatar da Kudirin.