A Lahadin nan ne majalisar gudanarwar kasar Sin, ta kafa wata tawagar musamman, domin binciken musabbabin mummunar fashewar da ta auku, a bakin wani shagon cin abinci dake wani titi mai yawan jama’a a birnin Yinchuan, fadar mulkin jihar Ningxia, dake arewa maso yammacin kasar Sin. An ce mai yiwuwa fashewar ta auku ne sakamakon yoyon fetur a ranar Laraba, inda ta hallaka mutane 31, tare da jikkata karin wasu mutanen 7.
Tawagar masu binciken da aka kafa ta gudanar da zamanta na farko da safiyar yau Lahadi, inda shugaban ta, kuma mataimakin ministan ayyukan agajin gaggawa Song Yuanming, ya kaddamar da tsare tsaren binciken, tare da gabatar da tanadin ayyukan da za a gudanar.
Song ya yi kira ga sassan masu ruwa da tsaki da su dora muhimmanci, wajen gano ainihin dalilin aukuwar ibtila’in ta amfani da kimiyya, da tantance wadanda ke da alhakin aukuwar lamarin, tare da gaggauta daukar matakan kawar da manyan hadurra masu nasaba da wurin da fashewar ta auku. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)