Majalisar dokokin jihar Kebbi ta zartar da ƙudirori guda biyu don gyara dokar ƙananan hukumomi ta 2008, da kuma ta kafa hukumar kula ƙananan hukumomin jihar.
An zartar da ƙudirin ne bayan yin la’akari da rahoton kwamitin majalisar kan harkokin ƙananan hukumomi da masarautu da kwamitin majalisar kan harkokin mulki da tsaro.
- Jam’iyyar PDP Ta Janye Daga Shiga Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kebbi
- PDP Ta Jajantawa Waɗanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Kebbi
Ƙudirin dokar da ya kafa hukumar yi wa ƙananan hukumomin jihar kebbi ya soke tare da sake kafa hukumar kula ma’aikata ƙananan hukumomin ta jihar Kebbi Cap 87 na shekarar 1996. Hukumar ce za ta sa ido kan harkokin yi wa kananan hukumomi aiki da sauransu.
‘Yan majalisar sun amince da dukkanin ƙudirori biyun bayan da shugaban majalisar, Muhammad Usman ya kaɗa ƙuri’a tsakanin mambobin majalisar.