Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Rano Muhammad Nazir Yau na tsawon watanni uku domin samun damar gudanar da bincike kan zarge-zargen rashin da’a, cin zarafi da kuma karkatar da wasu kudade da kansilolinsa suka yi masa.
Dakatarwar ta biyo bayan gabatar da rahoton wucin gadi na kwamitin majalisar kan kararrakin jama’a wanda shugaban masu rinjaye na majalisar, Hussaini Lawan Cediyar Yangurasa ya jagoranta, yayin zaman majalisar a ranar Laraba.
- NDLEA Ta Kama Dilolin Ƙwaya 49 A Kano
- Matatar Dangote Ta Sake Rage Farashin Man Fetur Zuwa N820 Kan Kowace Lita
Majalisar ta bukaci ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu da ta umurci mataimakin shugaban karamar hukumar ya maye gurbin shugabansa a matsayin riko, har sai an kammala bincike kan zargin.
Wasu daga cikin zarge-zargen da ake yi wa shugaban sun hada da kara farashin kudin takin gwamnati daga ₦20,000 zuwa ₦22,000 kan kowane buhu; hada rikici tsakanin shugabannin Siyasar yankin; raba kan Kansilolin karamar hukumar; tsunduma cikin harkokin siyasa masu raba kan jama’a ta hanyar bayar da dukiyar gwamnati ga abokan siyasarsa kawai; da dai sauransu.
Kwamitin majalisar, ya zauna da bangarorin biyu a ranar Talata, 12 ga watan Agusta inda shugaban ya yi watsi da wasu zarge-zargen da cewa, ba su da tushe balle makama, amma ya amince da karin farashin kudin takin gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp