Majalisar Dokokin Jihar Kano, ta taya Gwamna Abba Kabir Yusuf, murna bisa lashe lambar yabo ta LEADERSHIP a matsayin Gwamnan Shekara na 2024.
An ba shi wannan lambar yabo ne saboda ƙoƙarinsa wajen inganta harkar ilimi a jihar.
- Mata Sun Yi Zanga-zanga Kan Yawaitar Satar Mutane A Kogi
- Ku Kyautata Rayuwar Jama’a Ba Kan Kanku Ba — Buhari Ga Gwamnonin APC
Shugaban majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ya ce wannan lambar yabo ta nuna cewa an fara gano irin ƙoƙarin da Gwamna Yusuf ke yi a faɗin ƙasar nan.
Ya ce ƙudirin gwamnan na mayar da yara masu yawo a kan tituna zuwa makaranta yana kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar mutane.
Falgore, ya bayyana cewa manufofin gwamnatin Yusuf na bayar da ilimi kyauta da gyaran makarantu a sassa daban-daban na jihar na taimakawa wajen samar da ingantaccen yanayin koyo ga ɗalibai.
Ya tabbatar da cewa majalisar za ta ci gaba da mara wa shirye-shiryen da za su bunƙasa ilimi da jin daɗin al’umma baya.
Shugaban majalisar ya ƙara da cewa salon shugabancin gwamnan wanda ke ku8nshe da gaskiya da riƙon amana ya taimaka wajen amincewar jama’a ga gwamnati.
Ya ce Gwamna Yusuf jagora ne mai sauraron ƙorafin jama’a tare da himma wajen biyan buƙatunsu.
Ya buƙaci gwamnan da kada ya yi ƙasa a gwiwa wajen ci gaba da aikinsa duk da sukar da wasu ke masa.
Haka kuma ya shawarci sauran jami’an gwamnati da su kwaikwayi irin sadaukarwar gwamnan wajen yi wa al’umma aiki.
An gudanar da bikin bayar da lambar yabon ne a Abuja, inda aka yaba wa Gwamna Yusuf kan fifita ilimi, tallafa wa matasa da kuma inganta tafiyar da mulki.
Ana kallon nasarorinsa a matsayin abin koyi ga sauran jihohi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp