Majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) karo na 14 za ta fara zaman shekara-shekara karo na biyu a birnin Beijing a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024, a cewar shawarar da zaunannen kwamitin majalisar ya yanke a yau Juma’a. An yanke shawarar ne a karshen zaman zaunannen kwamitin NPC da aka gudanar daga ranar Litinin zuwa Juma’a.
Baya ga haka, an ba da shawarar fara zama karo na biyu na kwamitin majalisar ba da shawara kan kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14 (CPPCC) a ranar 4 ga watan Maris na 2024 a nan birnin Beijing. An bayar da shawarar ne a taron majalisar shugabanni na kwamitin CPPCC karo na 14 na baya-bayan nan.
- Xi Jinping Ya Gana Da Wakilan Da Suka Halarci Taron Tunawa Da Cika Shekaru 60 Da Kasar Sin Ta Fara Tura Ma’aikatan Agajin Jinya Ga Kasashen Waje
- CMG Ya Fitar Da Manyan Labaran Duniya Guda 10 Na 2023
A yau Juma’a ne zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin (NPC) ya kammala zama karo na bakwai a nan birnin Beijing.
A yayin rufe taron, ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da dokar kamfanoni da aka yi wa kwaskwarima, da dokar tabbatar da wadatar abinci, da gyara ta 12 (XII) ga dokar laifuffuka, da kuma yanke shawarar gyara dokar Sadaka.
Har ila yau, sun amince da nada Dong Jun a matsayin ministan tsaro, da cire Tang Dengjie daga mukamin ministan harkokin jama’a da nada Lu Zhiyuan kan mukamin, da kuma sauke Hu Heping daga mukamin ministan al’adu da yawon bude ido tare da nada Sun Yeli a mukamin.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rattaba hannu kan umarnin shugaban kasa guda biyar don sanar da dokokin da shawarwarin. (Yahaya)