Ƙungiyar ‘yan jarida ta Nijeriya (NUJ), reshen jihar Kano, ta mika sakon taya murna ga Ahmed Mu’azu bisa nadin da aka yi masa a matsayin mataimakin mai tsara dabara kan harkokin yada labarai a hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).
A matsayinsa na dan asalin jihar Kano, daukaka darajar Malam Mu’azu zuwa wannan matsayi abin alfahari ne ga masu aikin jarida a jihar.
- ‘Yansanda Sun Cafke Wani Matashi Ɗan Shekara 15 Da Ake Zargi Da Yin Fashi Da Makami A Gombe
- Majalisa Ta Amince Da Dokar Ɗaurin Rai Da Rai Ga Masu Yi Wa Ƙananan Yara Fyaɗe
Nadin nasa ya nuna aikin ƙwarewa da sadaukarwa a ɓangaren yaɗa labarai da yake da shi.
Mu’azu ya taɓa yin aiki a Sashen Hulda da Jama’a na Sashen Yada Labarai na NAHCON, inda ya nuna kwarewa ta musamman da kuma sadaukar da kai ga aikinsa na hulda da jama’a. Muna da yakinin cewa, kwarewarsa za ta kara habaka harkar yada labarai ta NAHCON da kuma karfafa kokarinta na hulda da jama’a.
Majalisar NUJ Kano na murnar wannan gagarumin naɗin tare da kwadaitar da Malam Mu’azu da ya ci gaba da kare martabar aiki, kwazo da hidima a sabon aikinsa.