Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA), ta samu lambar yabo ta kyautar gaskiya da riƙon amana ta shekarar 2025 daga Kwamitin Binciken Asusun Jama’a (PAC) na Majalisar Tarayya.
An ba da kyautar ne a matsayin girmamawa ga jajircewarta wajen bayyana gaskiya, sarrafa kuɗi, da bin ƙa’idodin lissafi.
- FRCN Ya Kaddamar Da Shirin Koyar Da Sinanci Mai Taken “Hello China”
- Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (2)
An gabatar da kyautar ne a wajen rufe taron kwana uku da aka gudanar a Abuja kan Asusun Jama’a da Sarrafa Kuɗi, wanda Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka shirya.
Taken taron shi ne: “Gudanar da Kuɗi a Nijeriya: Ƙirƙirar Sabuwar Hanyar Gaskiya Da Ci gaba Mai Ɗorewa.”
A jawabinsa, Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Wakilai, Hon. Bamidele Salam, ya yaba wa NPA saboda samar da tsarin bayani kan kuɗaɗenta da kuma goyon bayan hanyoyin bincike da gaskiya.
Shi ma Shugaban Kwamitin Asusun Jama’a na Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Wadada, ya bayyana cewa wannan kyauta alama ce ta gaskiya da amincewa da ayyukan hukumar.
Ya ce NPA ta nuna ƙwazo wajen bin ƙa’idojin lissafi da kuma tallafa wa hanyoyin bayyana gaskiya a ayyukan gwamnati.
Shugaban NPA, Dr. Abubakar Dantosho, wanda ya karɓi kyautar a madadin hukumar, ya sake tabbatar da ƙudirinsa na yin gyare-gyare da kuma tabbatar da gaskiya a dukkanin ayyukan hukumar.
Dr. Dantosho ya ƙara da cewa yin adalci da riƙon amana wajen harkokin kuɗi na daga cikin abubuwan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke da niyya a ƙarƙashin shirin “Renewed Hope”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp