Majalisar Wakilai Ta Amince Da Bukatar Shugaba Bola Tinubu Na Tara Jimillar Dala Biliyan 2.347 Daga Kasuwar Jari Ta Duniya Don cike giɓin kasafin kuɗi na 2025.
Amincewar ta biyo bayan la’akari da amincewa da rahoton da shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan taimako, lamuni, da bayar da bashi, Hon. Abubakar Hassan Nalaraba (APC, Nasarawa) ya gabatar a zaman Majalisar na ranar Laraba.
Rahoton kwamitin ya nuna cewa, an raba shirin bayar da lamunin zuwa ɓangarori biyu – Dala Biliyan 1.23 don cike giɓin kasafin kudi na 2025 da Dala Biliyan 1.12 don sake ba da kuɗi ga Asusun Bai Daya Na Nijeriya Wanda ya dace a saka kudin a watan Nuwamba, 2025.














