Yunkurin bunƙasa masana’antu da kamfanin Dangote ke yi a Nijeriya, ya sake samun ƙwarin gwiwa yayin da ‘yan majalisar tarayya ke marawa ci gaban kamfanin baya.
Yayin ziyarar da ‘Yan Majalisar Wakilai da suka kai Kamfanin Simintin Dangote da ke Obajana a Jihar Kogi, sun bayyana jin dadinsu kan irin gagarumin ƙoƙarin kamfanin a wajen samar da siminti a Nijeriya.
- Sin Da Afirka Aminai Ne Wajen Neman Zamanantar Da Kansu
- Minista Ya Nemi A Ƙara Ƙulla Danƙon Zumunci A Tsakanin Nijeriya Da Kamfanin BBC
Cikin jawabinsa yayin ziyarar, shugaban kwamitin kula da ma’adanai na majalisar, Gaza Jonathan Gbefwi, wanda shi ya jagoranci tawagarsa zuwa masana’antar simintin ya jaddada bukatar haɗin gwuiwa tsakanin mahukunta a Nijeriya, da masu zuba jari don bunƙasa masana’antun kasar nan.
Ya kara da cewa, kamfanin simintin Dangote ya buɗe hanya ta fuskar zuba jari da samar da ayyukan yi da samar da haraji, wanda ya ce hakan duk na daga cikin yunƙurin ganin Najeriya ta samu ci gaba ne.
Ya bayyana cewa, dalilin ziyarar da kwamitin ya kai shi ne binciken dalilan da suka haddasa tsadar siminti a faɗin ƙasar nan don samar da maslaha ga lamarin da ke ciwa yan ƙasa tuwo a kwarya.
Da yake mayar da jawabi ga ’yan majalisar game da farashin, Daraktan Rukunin Kamfanin Simintin Dangote, Engr Azad Nawabuddin ya bayyana cewa, kayayyakin da ake amfani da su wajen simintin ana sayo su ne da Dala iya duwatsu ne kawai ake samu a Nijeriya, ya wanda ya ce shine dalilin tashin gwauron zabin.
Kazalika ‘Yan majalisar sun ziyarci ɗayan kamfanin simintin Dangote da ke Okpella na jihar Edo inda Daraktan Ismail Muhammad, ya ce kamfanin ya zuba makudan kuɗaɗe wajen samar da kayayyakin kere-kere na zamani don a samu nasarar gudanar da aiki.