Majalisar wakilai, ta umarci babban bankin Nijeriya (CBN), da ya janye aiwatar da harajin tsaro na yanar gizo wanda za a ke cire kashi 0.5 daga asusun kwastomomin bankuna.
‘Yan majalisar sun bayyana matakin a matsayin abu mai wuyar gaske.
- Almundahana: Kotu Ta Bayar Da Belin Hadi Sirika Da ‘Yarsa
- Majalisar Dattawa Za Ta Kafa Dokar Kare Hakkin ‘Yan Aikatau A Nijeriya
Matakin na zuwa ne a matsayin martani ga wani kuduri kan bukatar gaggawa na dakatar da gyara aiwatar da harajin, wanda babban bankin ya gabatar a ranar Litinin.
A cewar majalisar, CBN ya janye takardar aiwatar da tsarin da ya fitar , sannan kuma ya fayyace tsarin yadda ‘yan Nijeriya za su fahimta babu cuta babu cutarwa.
Majalisar ta kuma nuna damuwa kan cewa za a aiwatar da dokar cikin kuskure idan ba a dauki matakin gaggawa ba, don magance matsalolin da ke tattare da umarnin da CBN ya bayar da kuma yadda ‘yan Nijeriya suka fassara shi.
Idan ba a manta ba a ranar Litinin ne CBN, ya fitar da sanarwar da ta umarci bankun da cibiyoyin hada-hadar kudi da su fara cire harajin.
Sai dai sanarwar ta haifar da rudani a tsakanin ‘yan Nijeriya, lamarin da ya sanya mutane fara tofa albarkacin bakinsu kan sanarwar.