A kokarinta na tabbatar da samun sauyi mai kyau a ayyukan makarantar, sabuwar shugabar da aka nada ta Makarantar Fasahar Kiwon Lafiya ta Kano, Hajiya Rakiya Mukhtar, ta kafa kwamitoci da za su binciki dukkan al’amuran makarantar da nufin samar da yanayi mai kyau da inganci ga dalibai.
Idan dai za a iya tunawa, ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar, ta nada Hajiya Rakiya Mukhtar a matsayin A.g Shugaban makarantar fasahar kiwon lafiya ta jihar a wasika mai lamba MOH/STAFF-S/T.II/I mai kwanan wata 9 ga Yuni, 2023 bayan sake fasalin shugaban cin makarantar.
Sakamakon kuka da bukatar da daliban suka gabatar kan zargin tabarbarewar harkokin makarantar yasa Hajiya Rakiya kafa kwamitocin da zasu sake nazari kan makarantar domin tsaftace tsarin tare da gyara zarge-zargen da ake yi wa shugabannin da suka gabata domin samun nasarar karbar ragamar aiki tare da ci gaba da gudanar da ayyukan makarantar cikin sauki.
Ta ci gaba da cewa, an kafa kwamitocin ne domin duba duk wasu matsalolin da daliban makarantar ke korafi akai, inda ta ce an yi hakan ne domin dawo da martabar makarantar da aka bata ba wai don bata suna ko farautar kowa ba.