• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Makarantu Masu Zaman Kansu Sun Koka Kan Kudaden Tafiyar Da Ayyukansu

by Idris Aliyu Daudawa
12 months ago
Makarantu

Masu ruwa da tsaki ta bangaren ilimi sun yi kira da a dauki tsari na gaggawa saboda  arage yawan kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da makarantu masu zaman kansiu.

Yomi Otubela ita ce shugaban kungiyar makarantu masu zaman kansu ta kasa ya yi jawabi ne kan irin tabarbarewar tattalin arziki wanda dalilin hakan makarantu masu zaman kansu suna ji a jikinsu.

  • Kamfanin Hakar Uranium Na Sin Ya Bayar Da Gudunmuwar Na’urori Ga Wata Makaranta A Namibia
  • An Kama Dillalin Safarar Makamai Dan Aljeria A Zamfara 

A hirar da tayi da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar lahadi, ya ce akwai bukatar da dauki tsare- tsare ba tare da bata lokaci ba, wadanda za s taimaka wajen saukaka kudin kayan karatu.

Otubela ya kara da cewar su tsare- tsaren ya dace su samar da wasu hanyoyi da za’a bar daukar haraji akan kudaden bashin da ake ba mabobin kungiyar.

Shugaban na kungiyar NAPPS yayi kira da hadin kai domin samun dama ta lamarin daya shafi fasaha.

LABARAI MASU NASABA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ya ci gaba da bayanin“Mun san cewa idan har aka samu tallafi daga gwamnatoci wadanda za’a ba makarantu masu zaman kansu,hakan zai sa su makarantu masu zaman kansu su rage fiye da yara milyan 18 wadanda basu zuwa makaranta a Nijeriya.”

Otubela ya kara jaddada cewa makarant da yawa karkashin kungiyar sun bullo da tsari na biyan kudin makaranta,inda take aiki tare da Iyayen yara, domin a tabbatar da cewa babu wani yaron da aka bari saboda Iyayen shin a fuskantar matsalolin da suka shafi kudi.

Kamar yadda yayi karin haske  kungiyar NAPPS tana yin iyakar kokarinta wajen samar da ilimi mai nagarta, da kuma sanin irin halin rayuwar da al’umma suke ciki, wajen bin lamarin hanyar data kamata.

“Muna fatan gwamnati zata kara kudaden taimakon da take badawa kan tsarie- tsaren horar da Malaman makaranta, da kuma sauran wasu nau’oin taimakon da ake badawa na kudade ga makarantu domin su inganta abubuwan more rayuwa a makarantu kamar yadda Otubela ya bayyana”.

“Hadin gwiwar ba wai abin zai tsaya bane kan taimakon matsalolin da makarantu masu zaman kansu ke fuskanta ba ne, har ma da tabbatar da kowane dalibin Nijeriya ba tare da la’akari yadda mahaifansa suke ba,ya samu ilimi mai nagarta.”

Segun Olayode wanda yana daya daga cikin Iyaye wanda shi masani ne kan kimiyyar data shafi lamarin kula da lafiya, cewa yayi ya kara kaimi ne domin ya biya karin kudin makarantar da aka yi na ‘ya’yan shi.

Wata mahaifiya ma wato, Tolani Odofin, wadda ita ma’aikaciyar gwamnati ce, tace ba zata iya biyan karin kudin makarantar ba, sai dai za ta mai da ‘ya;yanta wata makaranta.

Ta ce “Hukumar makarantar ta rubuta masu takarda lokacin huru inda aka bayyana masu  lamarin tabarbarewar tattalin arziki ne yasa aka yik arun kudin makarantar”.

Ta ce “Ni da mijina mun yanke shawarar sa su a wata  makaranta saboda ba za mu iya biyan sabon kudin makaranatar.Daga Naira 65,500  zuwa Naira 95,500, bayan haka kuma ga kudin littattafai da sauran kayan karatu sun karu”.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
Ilimi

NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu

November 8, 2025
gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
Next Post
Nazarin Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (15)

Nazarin Dabarun Koyarwa Da Amfaninsu (15)

LABARAI MASU NASABA

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

Soludo Ya Sake Lashe Zaɓen Gwamnan Anambra

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025
Triumph

Zargin Ɓatanci Ga Annabi: Alaƙar Triumph Da Gwamnatin Kano Da Majalisar Shura

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

Kasar Sin Ta Fitar Da Takardar Bayani Kan Samun Ci Gaba Mai Karancin Fitar Da Hayaki

November 8, 2025
Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

Kasar Sin Ta Sake Jaddada Cikakken Goyon Bayanta Ga Muhimmiyar Rawar Da MDD Ke Takawa A Harkokin Kasa Da Kasa 

November 8, 2025
Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

Turkiyya Na Karbar Bakuncin Wasu Kasashen Musulmai Game Da Makomar Gaza

November 8, 2025
Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

Babban Yankin Sin Da Taiwan Sun Yi Tarukan Bita Don Tunawa Da Taron Xi Da Ma Mai Tarihi

November 8, 2025
Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

Kasashen Afirka Bakwai Da Sojojin Amurka Suka Shiga

November 8, 2025
Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

Firaministan Kasar Georgia: CIIE Muhimmin Dandali Ne

November 8, 2025
Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

Yadda Aka Tsara Gudanar Da Gasar Kofin Afirka A Moroko

November 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.